Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Available in 54 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci.»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa masoyinsa kuma abokinsa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa wasicci kuma ya alkawaranta masa ɗabi'u uku: Na farko: Azimin kwana uku a kowane wata. Na biyu: Raka'a biyu ta walaha a kowace rana. Na uku: Witiri kafin bacci; hakan ga wanda ya ji tsoron kada ya farka a ƙarshen dare.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality