Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:

Available in 70 languages
«Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa Jibrilu bai gushe ba yana maimaita masa kuma yana umartarsa da kulawa da maƙoci, wanda shi ne makusancin gida, musulmi ne ko kafiri, ɗan uwa ne ko ba ɗan uwa ba ne, da kiyaye haƙƙinsa da rashin cutar da shi, da kyautatawa gareshi da haƙuri a kan cutarsa, har (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi zaton cewa daga girmama haƙƙin makoci da maimaitawar Jibrilu hakan cewa wahayi zai sauka da a ba shi (wani abu )daga dukiyar maƙocinsa wacce zai barta bayan mutuwarsa.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality