Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

Available in 55 languages
«Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna, kuma mutum ba zai gushe ba yana yin gaskiya, kuma yana kirdadon gaskiya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan gaskiya ne. Kuma na haneku da ƙarya, saboda ƙarya tana shiryarwa ne zuwa ga fajirci, kuma fajirci yana shiryarwa ne zuwa ga wuta, mutum ba zai gushe ba yana yin ƙarya kuma yana kirdadon ƙarya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan ƙarya".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da gaskiya, kuma ya bada labarin cewa lazimtarta yana kaiwa zuwa aiki na gari madawwami, mai lazimtar aikin alheri yana kai mai shi zuwa ga aljanna, ba zai gushe ba gaskiya tana mai maituwa ga reshi a boye da fili, kuma yana cancantar sunan mai yawan gaskiya; shi ne kai matuƙa a gaskiya, Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya tsawatar daga ƙarya da faɗar ƙarya; domin cewa ita tana kaiwa zuwa karkacewa daga daidai da kuma aikin sharri da ɓarna da saɓo, sannan ta kaishi zuwa wuta, ba zai gusheba yana yawaita ƙarya har sai an rubuta shi cikin maƙaryata a gurin Allah.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality