Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abdullahi Bn Amr -Allah Ya yarda da su- ya ce:

Available in 66 languages
«Daga Abdullahi Bn Amr -Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taɓa kasance wa mai alfasha ba, ko mai ƙoƙarin alfasha ba, ya kasance yana cewa: Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku.»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Mummunar magana ko mummunan aiki ba su kasance cikin dabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba, bai nufe shi ba, kuma bai ganganta yinsa ba, to, shi fa [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ma’abocin ɗabi’u ne masu girma. Kuma [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa: Lalle mafi falalarku a wurin Allah mafi kyawunku kyawawan ɗabi’u, ta hanyar bayar da abu mai kyau, da sakin fuska, da kamewa daga cutarwa, da juriya, da hulɗa da mutane da abu mai kyau.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality