Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ILIMIN AƘIDA

Daga Abdullahi ɗan Amru ɗan Ass - Allah Ya yarda da su -:

Available in 56 languages
«Daga Abdullahi ɗan Amru ɗan Ass - Allah Ya yarda da su -: Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina neman tsarin Allah Mai girma, da fuskarSa Mai girma, da sarautarSa daɗaɗɗiya, daga Shaiɗan abin jefewa", Ya ce: Wannan kawai? na ce: Eh, ya ce: Idan ya ce haka Shaiɗan zai ce : an kiyaye shi daga gareni ragowar yinin.»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga masallaci zai ce: (Ina neman tsarin Allah Mai girma) Ina neman tsari ina fakewa ga Allah da kuma siffofinSa (Da fuskarSa mai kyauta) Mai kyauta Mai bayarwa, (Da sarautarSa) RinjayenSa da ikonSa da rinjayenSa akan wanda ya yi nufi daga halittarSa (Madawwami) na tun fi azal na har abada (Daga Shaiɗan abin jefewa) Abin nisantarwa abin korewa daga rahamar Allah, Wato; Ya Allah Ka kiyayeni daga wasiwasinsa da halakarwarsa da tsarinsa da haɗarinsa da ƙawacensa da ɓatarwarsa, domin shi ne sababi a ɓatarwa mai sa halakarwa da jahilci, Aka cewa Abdullahi ɗan Amr "Shin shike nan?" Wato: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi wannan kadai? Ya ce: Eh. Idan mai shiga masallaci ya faɗi wannan addu'ar; Shaiɗan zai ce : Haƙiƙa an kiyaye ran wannan mai shigowar daga gareni dukkanin lokaci, yininsa da darensa.

Source
Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Download image

Saved at original quality