Hadith for the World
FIƘHU DA USULU

Haddodi

4 hadiths

4 hadiths

Ankarbo daga A'isha-Allah ya yarda da ita-"Cewa Kuraishawa lamarin Almakhzumiyya datai sata ya damesu,sai suka ce:Waye zai yiwa Manzan Allah tshira da amincin Allah su tabbata agareshi maganarta?,sai suka ce:Ba wanda zai iya tararsa sai Usama Dan Zaid Masoyin Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai Usama ya gaya masa,sai yace:ka nemi Ceto cikin Hukunci daga Hukunce-Hukuncen Allah?sannan ya tashi yayi huduba,sai yace:Hakika abinda ya halakar da wadanda suke gabaninku cewa su sun kasance idan wani Mai'alfarma daga cikinsu yayi sata sai su rabu dashi,idan kuma Mairauni ne acikinsu yayi sata sai su tsayar da Hukunci akansa,na rantse da Allah:da cewa Fadima yar Muhammad za tayi sata da lallai na yanke Hannunta".Awata ruwayar kuma"Wata Mace ta kasance tana arar kaya sai kuma ta musashi,sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi umarni da a yanke Hannunta"Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa sama".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya ɗaga makami a kammu, to, ba ya tare da mu"Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن أبي هريرة عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «لعن الله السارق، يسرق البَيْضَةَ فَتُقْطَعُ يده، ويسرِقُ الحَبْلَ فَتُقْطَعُ يَدُهُ».متفق عليه