Hadith for the World
Tsarki

Alwala

8 hadiths

8 hadiths

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskuren da ya yi kallo da shi da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa - ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa - idan ya wanke hannayen sa, kowane kuskure zai fita daga hannayen sa waɗanda hannayen sa suka damƙa tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa -, idan ya wanke ƙafafuwan sa kowane kuskuren da ƙafafuwan sa suka tafi gare shi zasu fita tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa - har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - da isnadi: “Idan kun sa shi, kuma idan kuna yin alwala, ku fara da kwanakinku.”Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
((An karbo daga Abi Huraira Allah ya yarda dashi yace Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:((Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al-kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala)).wanda ya sami damar tsawaita Farinsa daga gareku to ya aikata.Acikin wani Lafazi na Muslim:((Naga Aba Huraira yana Alwala,sai ya wanke Fuskarsa da Hannayensa har ya kusa isa Kafadunsa biyu,sannan ya wanke Kafafunsa biyu har saida ya daga izuwa Kaurinsa biyu,sannan yace:Na ji Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al'kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala))wanda ya sami damar tsawaita Farinsa da kyalkyalinsa to ya aikata.Kuma acikin wani lafazin na Muslim:Na ji Badadina-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:((Adon Mumini yana kaiwa inda Alwala takai((.Muslim ne ya rawaito shi duka Riwar ta sa biyun - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala"Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Usaman Bn Affan -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Laƙiɗ Bin Sabirah -Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance ɗan aiken Banul Muntafiƙi - ko a cikin jama'ar Bunul Muntafiƙi - zuwa wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Lokacin da muka zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bamu same shi agidansa ba, sai muka samu Nana A'isha uwar muminai, ya ce: Sai ta yi umarni a bamu farfesu, sai aka dafa mana, ya ce: Kuma aka zo mana da ƙina' - ƙina: Shi ne farantin da a cikinsa akwai dabino - sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: «‌Shin kun samu wani abu ne? ko shin an yi umarni akawo muku wani abu ne?» ya ce: Mukace: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da mai kiwo ya kora tumakansa zuwa garke, atare da shi akwai wani 'yar akuya tana kuka, sai ya ce: «‌Kai wane me aka haifa maka?», ya ce: 'Yar akuya, ya ce: «‌To ka yanka mana babbar akuya a madadinta», Sannan ya ce: «‌Kada ka zaci» bai ce: kada ka zaci «‌Mu saboda kaine muka yankata ba, muna da tumakai ɗari, bama so su ƙaru, idan aka haifawa makiyayin 'yar akuya, sai mu yanka babbar akuya a madadinta» Ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai ni ina da wata mata, akwai wani abu a harshenta - yana nufin bata iya magana ba - ya ce: «‌To ka saketa», ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai sahabiya ce, kuma ina da ɗa tare da ita, ya ce: «‌To ka umarceta» Yana cewa ka yi mata wa'azi, «‌Idan akwai alheri a tare da ita zata aikata, kada ka daki matarka kamar yadda kake dukan baiwarka», sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labari game da alwala, ya ce: «‌Ka cika alwala, ka tsettsefe tsakanin yatsu, ka kai matuƙa a kuskurar baki sai dai idan ka kasance mai azimi ne».Abu Dawud ya rawaito shi, da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah
Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".Muslim ne ya rawaito shi