Hadith for the World
ILIMIN AƘIDA

Imani da Hukuncin Allah da Qaddara

8 hadiths

8 hadiths

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi".Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Cewa shi ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah; Shin bana nuna maka wata mace daga cikin 'yan aljanna ba? na ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar da ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Ni ina farfaɗiya kuma inayin tsirara, to ka roƙamin Allah, ya ce: «‌Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki» ta ce: Zan yi haƙuri, ta ce : To cewa inayin tsirara to ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara, sai ya roƙa mata.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Anas Dan Malik -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi ya ce: "Lallai cewa Gwaggwaben lada yana tare da Girman Bala'i kuma cewa Allah Mai girma da Daukaka idan yaso Mutane to sai ya Jarrabesu, to duk wanda yarda da Jarrabawar to sai ya sami yardar Allah, kuma duk wanda yayi fushi to shi ma sai Allah yayi fushi da shi"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi
Daga ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, sai ya ce: "Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sameshi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa da al'umma za su taru a kan su amfaneka da wani abu, ba za su amfaneka ba sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta maka, da za su taru a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su cutar da kai ba, sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta a kanka, an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe".Tirmizi ne ya ruwaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwadayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana bude aikin Shaidan".Muslim ne ya rawaito shi
An karvo daga Abi Izza Al-huzali -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Idan Allah ya so karvar ran wani Bawansa a wata Qasa sai ya sanya wata buqata a can"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Al-Tayalisi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi dan Amr dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah Ya rubuta abinda ya kaddarawa halittu kafin Ya halicci sammai da kasa da shekara dubu hamsin, ya ce: Al’ArshinSa yana kan ruwa".Muslim ne ya rawaito shi
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِنَّ اللَّهَ قَالَ: إِذَا ابْتَلَيْتُ عَبْدِي بِحَبِيبَتَيْهِ فَصَبَرَ، عَوَّضْتُهُ مِنْهُمَا الجَنَّةَ» يُرِيدُ: عَيْنَيْهِ.رواه البخاري