Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Available in 60 languages
«Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mutumin da yake yaƙi dan jarumta, (da wanda) yake yaƙi dan ƙabilanci, (da wanda) yake yaƙi dan riya, wanne ne saboda Allah? sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

An tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga saɓanin manufofin masu yin yaƙi; wanda ya yi yaƙi dan jarumtaka ko ƙabilanci ko dan aga matsayinsa a cikin mutane ko wanin hakan, wannene saboda Allah? Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya yi yaƙi saboda Allah shi ne: Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality