Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ILIMIN AƘIDA

Daga Ummu al-Darda'i da Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbara agare shi - ya kasance yana cewa:

Available in 41 languages
«Daga Ummu al-Darda'i da Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbara agare shi - ya kasance yana cewa: «‌Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce, a daidai kansa akwai wani Mala'ika wanda aka wakilta a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce: Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin haka».»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa musulmi a bayan idon wanda aka yi wa addu'ar abar karɓa ce; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a cikin ikhlasi, kuma lallai cewa a wajen kan mai addu'ar akwai wani Mala'ikan da aka wakilta, a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce; Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin abinda ka roƙa.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality