Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ILIMIN AƘIDA

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

Available in 71 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki, Allah Ya la'anci mutanen da suka maida kaburburan Annabawansu masallatai".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya roki Ubangijinsa da kada Ya maida kabarinsa tamkar gunkin da mutane suke bauta masa ta hanyar girmama shi, da fuskantarsa a cikin sujjada, sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sanar da cewa Allah Ya nisantar Ya kore wanda ya maida kaburburan Annabawa masallatai daga rahamarsa' domin maida su masallatai sila ce zuwa bauta musu da kuma kudircewa a cikinsu.

Source
Ahmad ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality