Hadith for the World
Sallah

Hukunce Hukuncen Masallaci

9 hadiths

9 hadiths

Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku daidaita sahunku, don daidaita shahu na daga cikar sallah".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki, Allah Ya la'anci mutanen da suka maida kaburburan Annabawansu masallatai".Ahmad ne ya rawaito shi
عن أبي ذر رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم :«عُرِضَتْ عَلَيَّ أعمالُ أُمتي، حَسَنُهَا وسَيِّئُهَا فَوَجَدتُ في مَحَاسِنِ أَعْمَالِهَا الأَذَى يُمَاطُ عَنِ الطَّرِيقِ، ووَجَدتُ في مَسَاوِئِ أَعْمَالِهَا النُّخَاعَةُ تَكُونُ في المَسْجِدِ لا تُدْفَنُ».رواه مسلم
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Katada AsSulami - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Humaid ko daga Abu Usaid ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa".Muslim ne ya rawaito shi
عَن أَبي هُرَيْرَةَ، قَالَ: قَامَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي صَلاَةٍ وَقُمْنَا مَعَهُ، فَقَالَ أَعْرَابِيٌّ وَهُوَ فِي الصَّلاَةِ: اللَّهُمَّ ارْحَمْنِي وَمُحَمَّدًا، وَلاَ تَرْحَمْ مَعَنَا أَحَدًا. فَلَمَّا سَلَّمَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ لِلْأَعْرَابِيِّ: «لَقَدْ حَجَّرْتَ وَاسِعًا» يُرِيدُ رَحْمَةَ اللهِ.رواه البخاري
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi