Hadith for the World
Sallah

Zikirin Sallah

15 hadiths

15 hadiths

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yin addu'a yana cewa: "Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)". A cikin wani lafazin na Muslim: "Idan dayanku ya gama tahiyar karshe, to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da sharrin Mai yawan yawo makaryaci (Jujal).Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai ya yi shiru ɗan wani lokaci gabanin fara karatu, sai na ce: Ya manzon Allah, fansarka baba na da Baba ta, kana ganin shirun da kake yi tsakanin kabbara da karatu, me kake cewa? ya ce: Ina cewa: Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwan ƙanƙara kuma mai tsananin sanyi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannuna, sai ya ce: "Ya Mu'az, wallahi lallai ni ina sonka", sai ya ce: "Ina yi maka wasicci ya Mu'az bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa".Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shi
Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن عائشة رضي الله عنها أنّ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم كانَ يقول في ركوعه وسجودِه: «سبُّوحٌ قُدُّوسٌ رَبُّ المَلاَئِكَةِ وَالرُّوحِ».رواه مسلم
Daga Ka'ab dan Ujrah - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu".Muslim ne ya rawaito shi
عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه أنَّ رسولَ الله صلى الله عليه وسلم كان إذا قامَ إلى الصلاة، قال: «وَجَّهتُ وجهي للذي فطر السماوات والأرض حنيفًا، وما أنا من المشركين، إنَّ صلاتي، ونُسُكي، ومَحياي، ومماتي لله رب العالمين، لا شريك له، وبذلك أُمِرتُ وأنا من المسلمين، اللهمَّ أنت المَلِك لا إله إلَّا أنت، أنت ربي، وأنا عبدك، ظلمتُ نفسي، واعترفتُ بذنبي، فاغفر لي ذنوبي جميعًا، إنه لا يغفر الذنوب إلا أنت، واهدني لأحسن الأخلاق لا يهدي لأحسنها إلا أنت، واصرف عني سيئَها لا يصرف عني سيئها إلا أنت، لبَّيْك وسَعْدَيْك، والخيرُ كله في يديك، والشر ليس إليك، أنا بك وإليك، تباركتَ وتعاليتَ، أستغفرك وأتوب إليك»، وإذا ركع، قال: «اللهمَّ لك ركعتُ، وبك آمنتُ، ولك أسلمتُ، خشع لك سمعي، وبصري، ومُخِّي، وعظمي، وعَصَبي»، وإذا رفع، قال: «اللهم ربنا لك الحمد مِلءَ السماوات، ومِلءَ الأرض، ومِلءَ ما بينهما، ومِلءَ ما شئتَ من شيء بعد»، وإذا سجد، قال: «اللهم لك سجدتُ، وبك آمنتُ، ولك أسلمتُ، سجد وجهي للذي خلقه، وصوَّره، وشقَّ سمعَه وبصرَه، تبارك الله أحسنُ الخالقين»، ثم يكون من آخر ما يقول بين التشهُّد والتسليم: «اللهم اغفر لي ما قدَّمتُ وما أخَّرتُ، وما أسررتُ وما أعلنتُ، وما أسرفتُ، وما أنت أعلم به مني، أنت المُقَدِّم وأنت المؤَخِّر، لا إله إلا أنت».رواه مسلم
عن الحكم قال: غَلَب على الكُوفة رجُل -قد سَمَّاه- زَمَنَ ابن الأشْعَث، فأمر أبَا عُبيدة بن عبد الله أن يصلِّي بالناس، فكان يصلِّي، فإذا رَفع رأسه من الرُّكوع قام قَدْر ما أقُول: اللَّهُم ربَّنا لك الحَمد، مِلْءَ السَّماوات ومِلْءَ الأرض، ومِلْءَ ما شِئت من شَيء بعد، أهْل الثَّناء والمَجد، لا مانع لما أعْطَيت، ولا مُعْطِي لما مَنعت، ولا يَنفع ذَا الجَدِّ مِنْك الجَدِّ. قال الحَكم: فَذَكَرت ذلك لعَبد الرَّحمن بن أبي ليلى فقال: سمعت البَرَاء بن عَازب يقول: «كانت صلاة رسول الله صلى الله عليه وسلم وركُوعه، وإذا رفع رأسه من الرُّكوع، وسُجوده، وما بَيْن السَّجدتين، قريبًا من السَّوَاء» قال شُعبة: فذَكَرْتُه لِعَمرو بن مُرَّة فقال: قد رأيت ابن أبي ليلى، فلم تَكن صلاته هكذا.رواه مسلم
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Daga Sauban, Allah Ya yarda da shi: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya sallame daga sallah yana neman gafara sau uku, ya kuma ce: Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareka yake, Ka ɗaukaka ya ma’abocin girma da karamci . Walid ya ce: Na cewa Awza’i: Ya neman gafarar yake? Ya ce: Za ka ce ne: Ina neman gafarar Allah, ina neman gafarar Allah,Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, ya yi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan (lissafin) shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki ya tabbata gareShi, godiya ta tabbata gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai), za'a gafarta masa kurakuran sa, ko da sun kasance tamkar kumfar kogi".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Umamah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallar farilla to babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa".Nasa'i ne ya rawaito shi a cikin Al-Kubra
Daga Ibnu Abi Aufa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Allah Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa, cikar sammai da cikar ƙasa da cikar abin da ka so daga wani abu bayan nan"Muslim ne ya rawaito shi
عن ابن عمر قال: بينما نحن نصلي مع رسول الله صلى الله عليه وسلم إذ قال رجل من القوم: الله أكبر كبيرًا، والحمد لله كثيرًا، وسبحان الله بكرةً وأصيلًا، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «من القائلُ كلمة كذا وكذا؟» قال رجل من القوم: أنا، يا رسول الله. قال: «عجبتُ لها، فتحت لها أبواب السماء» قال ابن عمر: «فما تركتهن منذ سمعتُ رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول ذلك».رواه مسلم
عن أبي بكر الصديق رضي الله عنه: أنه قال لرسول الله صلى الله عليه وسلم: علمني دعاء أدعو به في صلاتي، قال: "قل: اللهم إني ظلمت نفسي ظلما كثيرا، ولا يغفر الذنوب إلا أنت، فاغفر لي مغفرة من عندك، وارحمني إنك أنت الغفور الرحيم".متفق عليه