Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su:

Available in 65 languages
«Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana yin Addu’a tsakanin sujjada biyu a Sallarsa, da waɗannan addu’o’in biyar, wacce Musulmi yake da matuƙar buƙatar su, kuma sun ƙunshi alheran duniya da lahira, kamar neman gafara, da ɓoye zunubi, da kuma yafe su, da malalo rahama da waraka daga shubuhohi da abubuwan sha’awe-sha’awe da rashin lafiya da cututtuka , da kuma roƙon Allah samun shiriya a kan gaskiya da kuma tabbata a kanta, da arziki na imani da ilimi da aiki na ƙwarai da kuma dukiya ta halal mai daɗi.

Source
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Download image

Saved at original quality