Hadith for the World
Sallah

Sifar Sallah

10 hadiths

10 hadiths

Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani : "(Tsarkakan) Gaisuwa ta tabbata ga Allah, da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne". Acikin wani lafazi na su: "Lallai cewa Allah Shi ne aminci, idan dayanku ya zauna a cikin sallah to ya ce: (Tarakakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agreka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah daalbarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari. Idan ya fadeta za ta samu kowanne bawan Allah nagari a sama da kasa, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonsa ne, sannan ya zabi abin yake so ya roka".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi: uwa ga Annabi "Idan Liman yace Ameen kuma kuce Ameen, domin duk wanda Ameen dinsa ta dace da Ameen din Mala'iku to angafarta masa abunda ya gabata na zunubansa.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه أنَّ رسولَ الله صلى الله عليه وسلم كان إذا قامَ إلى الصلاة، قال: «وَجَّهتُ وجهي للذي فطر السماوات والأرض حنيفًا، وما أنا من المشركين، إنَّ صلاتي، ونُسُكي، ومَحياي، ومماتي لله رب العالمين، لا شريك له، وبذلك أُمِرتُ وأنا من المسلمين، اللهمَّ أنت المَلِك لا إله إلَّا أنت، أنت ربي، وأنا عبدك، ظلمتُ نفسي، واعترفتُ بذنبي، فاغفر لي ذنوبي جميعًا، إنه لا يغفر الذنوب إلا أنت، واهدني لأحسن الأخلاق لا يهدي لأحسنها إلا أنت، واصرف عني سيئَها لا يصرف عني سيئها إلا أنت، لبَّيْك وسَعْدَيْك، والخيرُ كله في يديك، والشر ليس إليك، أنا بك وإليك، تباركتَ وتعاليتَ، أستغفرك وأتوب إليك»، وإذا ركع، قال: «اللهمَّ لك ركعتُ، وبك آمنتُ، ولك أسلمتُ، خشع لك سمعي، وبصري، ومُخِّي، وعظمي، وعَصَبي»، وإذا رفع، قال: «اللهم ربنا لك الحمد مِلءَ السماوات، ومِلءَ الأرض، ومِلءَ ما بينهما، ومِلءَ ما شئتَ من شيء بعد»، وإذا سجد، قال: «اللهم لك سجدتُ، وبك آمنتُ، ولك أسلمتُ، سجد وجهي للذي خلقه، وصوَّره، وشقَّ سمعَه وبصرَه، تبارك الله أحسنُ الخالقين»، ثم يكون من آخر ما يقول بين التشهُّد والتسليم: «اللهم اغفر لي ما قدَّمتُ وما أخَّرتُ، وما أسررتُ وما أعلنتُ، وما أسرفتُ، وما أنت أعلم به مني، أنت المُقَدِّم وأنت المؤَخِّر، لا إله إلا أنت».رواه مسلم
عن الحكم قال: غَلَب على الكُوفة رجُل -قد سَمَّاه- زَمَنَ ابن الأشْعَث، فأمر أبَا عُبيدة بن عبد الله أن يصلِّي بالناس، فكان يصلِّي، فإذا رَفع رأسه من الرُّكوع قام قَدْر ما أقُول: اللَّهُم ربَّنا لك الحَمد، مِلْءَ السَّماوات ومِلْءَ الأرض، ومِلْءَ ما شِئت من شَيء بعد، أهْل الثَّناء والمَجد، لا مانع لما أعْطَيت، ولا مُعْطِي لما مَنعت، ولا يَنفع ذَا الجَدِّ مِنْك الجَدِّ. قال الحَكم: فَذَكَرت ذلك لعَبد الرَّحمن بن أبي ليلى فقال: سمعت البَرَاء بن عَازب يقول: «كانت صلاة رسول الله صلى الله عليه وسلم وركُوعه، وإذا رفع رأسه من الرُّكوع، وسُجوده، وما بَيْن السَّجدتين، قريبًا من السَّوَاء» قال شُعبة: فذَكَرْتُه لِعَمرو بن مُرَّة فقال: قد رأيت ابن أبي ليلى، فلم تَكن صلاته هكذا.رواه مسلم
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai: Akan goshi sai ya yi nuni da hannunsa akan hancinsa, da hannaye, da gwiwoyi, da gefunan diga-digai, kuma kada ka tufke tufafi ko gashi".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Daga Anas -Allah ya yarda da shi- Lallai cewa Manzon Allah SAW ya kasance baya Al-qunuti sai in zai Addu'a ga wasu Mutane, ko yayi Addu'a kan wasu MutaneIbn Khuzaimah ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta".Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi
Daga Ibnu Abi Aufa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Allah Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa, cikar sammai da cikar ƙasa da cikar abin da ka so daga wani abu bayan nan"Muslim ne ya rawaito shi
Daga usman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi -: Lallai ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai haƙiƙa Shaiɗan ya shiga tsakanina da sallata da kuma karatuna, yana rikitar da ni, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku", sai ya ce: Sai na aikata hakan sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.Muslim ne ya rawaito shi