Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga Ibnu Abi Aufa - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Available in 63 languages
«Daga Ibnu Abi Aufa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Allah Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa, cikar sammai da cikar ƙasa da cikar abin da ka so daga wani abu bayan nan"»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u a sallah yana cewa: Allah Ya ji wanda ya gode maSa", wato: Cewa wanda ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - Allah - Maɗaukakin - sarki Ya amsa masa, Ya karɓi godiyarsa kuma Ya saka masa, sannan ya godewa Allah da faɗinsa; "Ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata a greKa, cikon sammai da cikon ƙasa da cikon abin da Ka so daga wani abu bayan nan", godiyar da za ta cika sammai da ƙassai da abin da ke tsakaninsu, kuma ya cika abin da Allah Ya so daga wani abu.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality