Hadith for the World
Sallah

Kusakuren Masu Sallah

5 hadiths

5 hadiths

Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida).Muslim ne ya rawaito shi
Daga Anas bn Malik - Allah ya yarda da shi - cewa Annabi -SAW- ya ga Kaki a Al-kibla, don haka yana da wahala gare shi har sai da aka ganshi a fuskarsa, don haka sai ya tashi ya goge da hannunsa. Tsakaninsa da Kibla, ba ɗayanku ya tofa albarkacin bakinsa, sai a hagu ko a ƙasan ƙafafunsa. ”Sa’annan ya ɗauki ƙarshen tufafinsa, ya tofa a ciknsa, sa’annan wasunku suka amsa, suka ce:“ Ko ya aikata hakan. ”Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Meke damun wasu mutane ne suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallarsu". Sai maganrasa ta yi tsanani a kan hakan, har ya ce: "Kodai su hanu daga hakan ko a fauce magannansu".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan: {Ku tsai da sallah domin tunani} [Daha: 14".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta".Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi