Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce:

Available in 60 languages
«Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani : "(Tsarkakan) Gaisuwa ta tabbata ga Allah, da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne". Acikin wani lafazi na su: "Lallai cewa Allah Shi ne aminci, idan dayanku ya zauna a cikin sallah to ya ce: (Tarakakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agreka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah daalbarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari. Idan ya fadeta za ta samu kowanne bawan Allah nagari a sama da kasa, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonsa ne, sannan ya zabi abin yake so ya roka".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - Tahiyar da ake fada a cikin sallah, hakika ya sanya hannunsa a cikin hannayensa, dan ya karkato da hankalin Dan Mas'ud gare shi, kamar yadda yake sanar da shi sura daga Alkur’ani abinda yake nuni akan kulawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wannan Tahiyar lafazi da ma'ana. Sai ya ce: "(Tsarkakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah": Su ne kowacce magana ko aiki mai shirayrwa akan girmamawa, dukkaninsu ababen cancantane ga Allah - Mai girma da daukaka -. "Salloli": Ita ce sananniyar sallah ta farilla da ta nafila, sun tabbata ga Allah - Madaukakin sarki -. "Tsarkakan Maganganu": Su ne maganganu da ayyuka da siffofi tsarkaka masu nuni akan cika, dukkaninsu ababen cancanta ne ga Allah - Madaukakin sarki -. "Aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa': Addu'ace gare shi da aminta daga dukkanin cututtuka da abin ki, da kari da yawaita a kowanne alheri. "Aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari": Addu'ace da aminta daga mai sallah da kuma kowanne bawa na gari a sama da kasa. "Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah': Wato ina tabbatarwa tabbatarwa a yanke cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. "Kuma cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne": Ina tabbatarwa a gare shi da bauta da Manzanci na karshe. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwadaitar da mai yin sallah ya zabi abinda yaso na addu'a ya roka.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality