FIƘHU DA USULU
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Available in 60 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai ya yi shiru ɗan wani lokaci gabanin fara karatu, sai na ce: Ya manzon Allah, fansarka baba na da Baba ta, kana ganin shirun da kake yi tsakanin kabbara da karatu, me kake cewa? ya ce: Ina cewa: Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwan ƙanƙara kuma mai tsananin sanyi".»Meaning translation ·
Saved at original quality








