FIƘHU DA USULU
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
Available in 43 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».»Meaning translation ·
Saved at original quality







