Hadith for the World
Faxakarwa da Wa’azozi

Tsarkake Zuciyoyi

9 hadiths

9 hadiths

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi".Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Daga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini ,idan abin farinciki ne ya same shi sai ya gode wa Allah sai, sai ya zamar masa alheri, idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zamar masa alheri’’.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare hanya", Ibnu Umar ya kasance yana cewa: Idan ka kai maraice to kada ka saurari safiya, idan ka wayi gari to kada ka saurari yammaci, ka yi riƙo daga lafiyarka dan rasshin lafiyarka, kuma daga rayuwarka dan mutuwarka.Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalince shi kuma kada ya ƙi taimakonsa, kada ya wulaƙanta shi tsoron Allah a nan yake" - ya yi nuni zuwa ƙirjin sa, sau uku - "Ya ishi mutum sharri ya wulaƙanta ɗan uwansa Musulmi, kowane Musulmi akan Musulmi haramun ne (ya zubda) jininsa, da dukiyarsa da mutuncinsa". Mutuncinsa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, hakan zai sa (ku godewa Allah) ba za ku raina ni’imominSa gareku ba».Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ni'imomi biyu ana yi wa da yawa daga mutane kamunga a cikinsu: Lafiya da rarar lokaci".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Sufyan Dan Abdullah AlSakafi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".Muslim da Ahmad ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi