HA
Faxakarwa da Wa’azozi
Ayyukan Zukata
14 hadiths
Ayyukan Zukata
14
Zuhudu da tsantseni
2
Halayen Mutane na Qwarai
4
Zargin Savo
6
Zargin Son Duniya
8
Zargin Son Rai da Sha'awoyi
1
Tuba
3
Tsarkake Zuciyoyi
9
Sifar Al-janna da Wuta
17
14 hadiths
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?" Ya ce: Babu komai, sai dai ni ina son Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce; "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Bamu taba farin ciki da wani abu ba, irin farin cikinmu da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Ni ina son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma ina kaunar in kasance tare da su dan son da nake musu, koda ban yi aiki irin aikinsu ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Ni ne mafi wadatar abokanan tarayya daga shirka, duk wanda ya aikata wani aiki ya hada ni da wani a aikin to Zan bar shi da shirkarsa".
Muslim ne ya rawaito shi
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin wafatinsa da (kwana) uku yana cewa: "Lallai kada ɗayanku ya mutu sai yana kyautatawa Allah zato".
Muslim ne ya rawaito shi
Daga Nawwas ɗan Sam'an alAnsari - Allah Ya yarda da shi ya ce: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga aikin alheri da kuma zunubi, sai ya ce: "Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma kaƙi mutane su yi tsinkaye akansa".
Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku".
Muslim ne ya rawaito shi
Daga Umar dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan ayyuka (ba sa inganta) sai da niyya, kaɗai mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne, wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da manzonsa, to, hijirarsa tana ga Allah da manzonsa, wanda hijirarsa ta kasance don duniya da zai sameta, ko wata mace da zai aureta, to, hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gareshi". A wani lafazin na Bukhari; "Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyyoyi, kaɗai kowane mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwadayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana bude aikin Shaidan".
Muslim ne ya rawaito shi
Daga Iyad ɗan Himar ɗan uwan Mujashi'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu yana mai yin huɗuba, sai ya ce: Sai ya koro hadisin kuma a cikinsa: «Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahari, kuma kada wani ya zalinci wani».
Muslim ne ya rawaito shi
An karbo daga Anas Allah Ya yarda da shi, ya ce: Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Imanin ɗayanku ba ya cika har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi sama da babansa da ‘ya’yansa da mutane bakiɗaya.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah SAW ya ce: "Mutane Kamar Ma'adanan Zinare da Azurfa ne, Mafifitanku a Jahiliyya sune Mafifitanku a musulunci idan Sukai Ilimi, Kuma Rayuka Kamar Rundunar yaki ce, duk wanda suka San juna sai su Saba, wanda kuma suka saba kuma sai suki jituwa" kuma an rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- Manzon Allah ya ce: "Zaku samu Mutane Kamar ne, Mafifitanku a Jahiliyya sune Mafifitanku a musulunci idan Sukai Ilimi, Kumazaku samu zababbu a cikin Mutane a wannan Al-amari su ne Mafiya tsananin kinsa, kuma zaku samu Mafi Sharrin Mutane Masu fuska biyu, wanda zai zowa wadan nan da wata fuska kuma wadan nan da wata Fuskar daban"
Buhari da Muslim suka rawaito shi da ruwayoyin sa
An rawaito daga Abdullahi Bn Akim -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi "Duk wanda ya danfaru da wani abu to za'a jibanta shi zuwa gare shi"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
عن ابن عباس حسبنا الله ونعم الوكيل: «قالها إبراهيم عليه السلام حين أُلقي في النار، وقالها محمد صلى الله عليه وسلم حين قالوا: {إن الناس قد جمعوا لكم فاخشوهم فزادهم إيمانا، وقالوا: حسبنا الله ونعم الوكيل} [آل عمران: 173]».
رواه البخاري
عن جابر قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إذا قضى أحدكم الصلاة في مسجده فليجعل لبيته نصيبًا من صلاته، فإن الله جاعلٌ في بيته من صلاته خيرًا».
رواه مسلم
Daga Ummu Salamah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi, sai ya faɗi abinda Allah Ya umarce shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai cewa mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], ya Allah Ka bani lada a cikin wannan musibar tawa kuma Ka musanya mini da mafi alheri da ita, sai Allah Ya musanya masa da mafi alheri daga ita", ta ce: Lokacin da Abu Salama ya rasu na ce: Waye a cikin musulmai ya fi Abu Salama alheri? farkon gidan da ya yi hijra zuwa ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan sai na faɗeta (addu'ar), sai Allah Ya maye mini gurbinsa da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Muslim ne ya rawaito shi