Hadith for the World
Faxakarwa da Wa’azozi

Sifar Al-janna da Wuta

17 hadiths

17 hadiths

Daga Ubada - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma Annabi Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne kalmarSa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare Shi, kuma aljanna gaskiya ce haka wuta ma gaskiya ce, Allah Zai shigar da shi Aljanna akan aikin da yake akansa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Aljanna ita ce mafi kusa daga dayanku daga igiyar takalminsa, wuta ma tamkar hakan".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Akwai matakai dari a cikin Aljanna da Allah ya tanadar wa mujahidai a tafarkin Allah, tsakanin sahu biyu kamar tsakanin sama da kasa."Buhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi», sai Abu Sa'id ya yi mamaki gareta (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaitata mini ya Manzon Allah, sai ya maimaita, sannan ya ce: «Ɗayar kuwa za'a ɗaukakawa bawa daraja ɗari da ita a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja biyu kamar tsakanin sama da ƙasa ne». Ya ce: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: «Jihadi a tafarkin Allah, jihadi a tafarkin Allah».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Anas bn Malik - yardar Allah ta tabbata a gare shi - da isnadi: “Za a zo da mafi alherin mutanen wannan duniya daga mutanen wuta ranar tashin kiyama, kuma za a rina su a cikin Wuta, sa’an nan a ce: Ya kai ɗan Adam, shin ka taɓa ganin abu mai kyau? ka taba rayuwa cikin jin dadi? Yana cewa: A'a, Wallahi, Ya Ubangiji, kuma mafi tsananin mutane a duniya za a kawo su ne daga 'yan Aljanna, sannan a rina a cikin Aljanna, sai a ce masa: Ya dan Adam, shin ka taba ganin wahala? Shin kun taɓa shan wahala? Yana cewa, "A'a, Wallahi ban taba ganin wahala ba, kuma ban taba ganin wahala ba."Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abdullah bn Masoud - Allah ya yarda da shi - tare da rahoto: "Za a shigar da Jahannama a wannan rana a kansa saboda iyayengiji dubu saba'in, tare da kowace sarauta ta sarakuna dubu saba'in da suke jan ta."Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u", kuma an tambayeshi game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane wuta sai ya ce: "Baki da farji".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- yace: "Saihan da Jihan da Furat da Nil baki xayan su kogunan Al-janna ne"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Sa'id al-Khudri da Abu Hurarira - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mai kira zai kira: Lallai cewa ku zaki yi lafiya ba za ku yi masassara ba har abada, kuma ku zaku rayu ba za ku mutu ba har abada, kuma cewa ku zaku samartaku ba zaku tsufaba har abada, kuma cewa ku zaku ni'imtu ba zaku yanke ƙauna ba har abada' wannan faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -: {Sai a yi kira cewa wancananku aljanna an gadar muku da ita saboda abinda kuka kasance kuna aikatawa} [al-A'araf: 43].Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Zai cewa 'yan aljanna: Yaku 'yan aljanna? sai su ce: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, sai Ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Dan me ba zamu yarda ba alhali Ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarKa ba? Sai Ya ce: Ni zan baku mafifici daga hakan, sai su ce: Ya Ubangiji, wane abu ne maffifici daga hakan? Sai Ya ce: Zan saukar muku da yardata, ba zan yi fushi daku ba a bayansa har abada".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai mumini yana da wata shema a cikin aljanna ta lu'ulu'u ɗaya mai ƙofa a cikinta, tsawonta mil sittin ne, mumini yana da mata a cikinta, mumini zai kewayesu amma sashinsu ba zai ga sashi ba".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Sa'ida Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita zuwa wurin da ake sallah, a babbar sallah ko a ƙarama, sai ya wuce inda mata suke, sai ya ce: "Yaku wannan mata, ku yi sadaka, dan ni an nuna min cewa kune mafi yawan 'yan wuta". Sai suka ce: Dan me ya Manzon Allah? ya ce: "Kuna yawaita tsinuwa, kuma kuna butulcewa zamantakewa, banga masu tawayar hankali da Addini mafi tafiyar da hankalin namiji ba mai karfin niyya kamar ɗayanku ba", suka ce: To menene tawayar Addininmu da hankalinmu ya Manzon Allah? ya ce: "Shin yanzu bai zama cewa shaidar mace kwatankwacin rabin shaidar namiji ba ce" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar hankalinta, shin yanzu idan ta yi al’ada ba ta sallah ba ta azimi" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar Addininta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Na tanadarwa bayiNa na gari, abinda wani ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, kuma bai taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani ɗan Adam ba» Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Wata rai ba ta sanin abinda aka ɓoye musu na abinda rai yake farin ciki da shi} [al-Sajdah: 17].Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Ayyad bin Hamar Al-Maja'a'i - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana a cikin hudubarsa: "A'a, Ubangijina Ya yi umarni ni in koya muku abin da kuka jahilta. Barorina dukkansu Hanafiyya ne, kuma aljannu ne suka zarge su, don haka na kutsa musu game da addininsu, kuma na hana su aikata abin da na yardar musu, kuma na umarce su da su yi tarayya da ni kamar yadda muddin ban sauko da iko ba, kuma Allah ya kalli mutanen duniya, sai larabawarsu da azzalumai suka kyamace su, ban da ragowar Ahlul Kitabi, sai ya ce: Kai, kuma na yi wahayi zuwa gare ka littafin da ruwa bai wanke shi ba, ka karanta shi yana bacci kuma a farke, kuma Allah ya umarce ni da in kona wani Kuraishawa. mai sasantawa, kuma mutum ne mai jin kai da tausasa zuciya ga kowane dangi kuma Musulmi, kuma mai kamun kai, mai tsafta, tare da 'ya'ya. kuma baya tuba C amma yana yaudarar ku ne a madadin danginku da mai shi «kuma ya ambaci» ɓatanci ko ƙarya da ɓatanci ».Muslim ne ya rawaito shi
عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما أنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «عُذِّبت امرأة في هِرَّة سَجَنَتْها حتى ماتت، فدخلت فيها النار، لا هي أطعمتها ولا سَقتها، إذ حبستها، ولا هي تَركتْها تأكل مِن خَشَاشِ الأرض».متفق عليه
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wutarku wani yankine daga yanki saba'in daga wutar Jahannama", (Sai) aka ce: Ya Manzon Allah, ta kasance ta isa (dan azabtarwa), ya ce: "An fifita ta a kansu da yanki sittin da tara, kowannen su tamkar zafinta yake”.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَبِرَسُولِهِ، وَأَقَامَ الصَّلاَةَ، وَصَامَ رَمَضَانَ كَانَ حَقًّا عَلَى اللَّهِ أَنْ يُدْخِلَهُ الجَنَّةَ، جَاهَدَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَوْ جَلَسَ فِي أَرْضِهِ الَّتِي وُلِدَ فِيهَا»، فَقَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَفَلاَ نُبَشِّرُ النَّاسَ؟ قَالَ: «إِنَّ فِي الجَنَّةِ مِائَةَ دَرَجَةٍ، أَعَدَّهَا اللَّهُ لِلْمُجَاهِدِينَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ، مَا بَيْنَ الدَّرَجَتَيْنِ كَمَا بَيْنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ، فَإِذَا سَأَلْتُمُ اللَّهَ فَاسْأَلُوهُ الفِرْدَوْسَ، فَإِنَّهُ أَوْسَطُ الجَنَّةِ وَأَعْلَى الجَنَّةِ -أُرَاهُ- فَوْقَهُ عَرْشُ الرَّحْمَنِ، وَمِنْهُ تَفَجَّرُ أَنْهَارُ الجَنَّةِ».رواه البخاري