Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Available in 70 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u", kuma an tambayeshi game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane wuta sai ya ce: "Baki da farji".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - yana bayyana cewa mafi giman sabubban da suke shigar da mutane aljanna sabubba biyu ne, sune: Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u. Tsoron Allah: Shi ne ka sanya kariya tsakaninka da tsakanin azabar Allah, ta hanyar aikata umarninsa da nisantar hane-hanensa. Kyakkyawar ɗabi'a: Tana kasancewa ne da shinfiɗar fuska, da yin aikin kirki, da kamewa daga cuta. Kuma mafi girman sabubban da suke shigarwa wuta sabubba biyu ne, su ne: Harshe da farji. yana daga saɓon harshe: Ƙarya, da raɗa, da annamimanci da wasunsu. Yana daga saɓon farji: Zina da luwaɗi da wasunsu.

Source
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Download image

Saved at original quality