Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana Addu’a da waɗannan kalomin:

Available in 53 languages
«Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana Addu’a da waɗannan kalomin: "Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga wasu al'amra: Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsari) ina fakewa ina dogara (da Kai) bada wanin Ka ba, (daga rinjayar bashi) da rinjayarsa da baƙin cikinsa da takaicin sa, ina roƙonKa taimako akan biyansa da warware shi. Na biyu: (Rinjayar maƙiyi) da rinjayansa da ɗora shi akaina, ina roƙon Ka kame cutarsa, da nasararsa a kansa. Na uku: (Dariyar maƙiya) da farin cikin makiya akan abinda yake samun musulmai na bala'i da musiba.

Source
Nasa'i ne ya ruwaito shi da Ahmad
Download image

Saved at original quality