Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:

Available in 69 languages
«Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Addu'a ita ce ibada', sannan ya karanta; " {Ubangijinku Ya ce ku roƙeni zan amsa muku, lallai waɗanda suke girman kai game da bautata za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu} [Gafir: 60].»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa addu'a ita ce ibada, to, wajibi ne ta zama dukkaninta abar tsarkakewa ga Allah, duka ɗaya ne, ta kasance addu'ar tambaya ce da nema, da ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - abin da zai amfaneshi, da tunkuɗe abin da zai cutar da shi a duniya da lahira, ko addu'ar ibada, ita kuma itace dukkanin abin da Allah Yake sonsa kuma Ya yarda da shi na maganganu da ayyuka na zahiri da baɗini, ibadu na zuciya ko na jiki ko na dukiya. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kafa dalili akan haka ta inda ya ce: Allah Ya ce: {Ku roƙeni zan amsa muku, lalle waɗanda suke girman kai game da bauta min, da sannu za su shiga jahannama suna ƙasƙantattu}.

Source
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Download image

Saved at original quality