Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Iyad ɗan Himar ɗan uwan Mujashi'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu yana mai yin huɗuba, sai ya ce: Sai ya koro hadisin kuma a cikinsa:

Available in 40 languages
«Daga Iyad ɗan Himar ɗan uwan Mujashi'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu yana mai yin huɗuba, sai ya ce: Sai ya koro hadisin kuma a cikinsa: «‌Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahari, kuma kada wani ya zalinci wani».»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe a cikin sahabbansa yana mai huɗuba, ya kasance daga cikin abinda ya ce: Lallai cewa Allah Ya yi masa wahayi cewa ya wajaba akan mutane su yi tawali'u a tsakaninsu, hakan ta hanyar ƙanƙar da kai ga halitta da tausasa lamura, har kada wani ya yi alfahari ta hanyar da'awar girma da kafafa da ɗaukakar da zai danganta kansa ko dukiyarsa ko wanin haka akan wani, kuma kada wani ya zalinci wani, kuma kada ya yi ta'addaci akan wani.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality