FALALOLI DA LADUBBA
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su- ya ce:
Available in 54 languages
«Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana barin waɗannan addu'o'i ba lokacin da ya yi yammaci ko ya wayi gari: "Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira, ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwami da lafiya a Addini na da duniya ta da iyalaina da dukiyata, ya Allah Ka suturta al'aurata - ko: al'aurorina Ka amintar da tsorona, ya Allah Ka kiyayeni ta gabana, da bayana, da damana, da haguna, da samana, ina nemn tsarinKa kada a yaudareni da kisa ta ƙarƙashina".»Meaning translation ·
Saved at original quality








