Hadith for the World
Faxakarwa da Wa’azozi

Zargin Son Duniya

8 hadiths

8 hadiths

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa duniya mai zakice koriya, kuma Allah Mai gadar daku ne a cikinta, sai ya duba yaya zaku yi aiki, don haka ku ji duniya kuma ku kiyayi mata, domin cewa farkon fitinar Banu Isra'ila ta kasance a mata ne".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Sahl n Sa'ad Al-Sa'idi -Allah ya yarda da shi- Manzon Allah SAW ya ce: "Da ace Duniya tana da kimar Fuffuken Saura, da Kafiri bai sha Ruwa Makwarwa daya ba a cikinta"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi
Daga Anas, Allah ya yarda da shi, da isnadi: “Uku za su bi mamaci: danginsa, dukiyarsa da aikinsa, sa’an nan biyu ya dawo daya ya rage: danginsa da kudinsa za su dawo, kuma aikinsa ya kasance”Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Khaulat Al-Ansariyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai wasu mutane suna kutsawa a dukiyar Allah ba tare da wani haƙƙi ba, to, wuta ta tabbata a garesu ranar al-ƙiyama".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Haƙiƙa wanda ya miƙa wuya (ga Ubangijinsa), kuma aka azurta shi da abu kaɗan (gwargwadan buƙatarsa), kuma Allah Ya wadata shi da abin da Ya ba shi to ya rabauta».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Zuciyar babba ba zata gushe ba tana budurwa a kan abubuwa biyu: A son duniya da tsawon buri".Bukhari ne ya rawaito shi