Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

Available in 47 languages
«Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi», sai Abu Sa'id ya yi mamaki gareta (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaitata mini ya Manzon Allah, sai ya maimaita, sannan ya ce: «Ɗayar kuwa za'a ɗaukakawa bawa daraja ɗari da ita a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja biyu kamar tsakanin sama da ƙasa ne». Ya ce: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: «Jihadi a tafarkin Allah, jihadi a tafarkin Allah».»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bawa Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - labarin cewa wanda ya yi imani da Allah kuma ya yarda da Shi a matsayin Ubangiji abin bauta kuma shugaba kuma mai umarni, kuma da Musulunci a matsayin Addini dan jawuwa da miƙa wuya da dukkanin umarce-umarcensa da hane-hanensa, da kuma (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da dukkan abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi; to aljanna ta tabbata gareshi, sai Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki ga (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaita mini ita ya Manzon Allah, sai ya aikata, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kuma ina da wata dabi'ar daban wacce Allah Yake daukaka darajar bawa da ita sau dari a cikin aljanna, tsakanin kowace darajoji biyu kamar tsakanin sama da kasa ne, Abu Sa'ida ya ce: Waccece ya Manzon Allah? ya ce: Jihadi a tafarkin Allah, jihhadi a tafarkin Allah.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality