ILIMIN AƘIDA
Daga Ummu Salamah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
Available in 39 languages
«Daga Ummu Salamah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi, sai ya faɗi abinda Allah Ya umarce shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai cewa mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], ya Allah Ka bani lada a cikin wannan musibar tawa kuma Ka musanya mini da mafi alheri da ita, sai Allah Ya musanya masa da mafi alheri daga ita", ta ce: Lokacin da Abu Salama ya rasu na ce: Waye a cikin musulmai ya fi Abu Salama alheri? farkon gidan da ya yi hijra zuwa ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan sai na faɗeta (addu'ar), sai Allah Ya maye mini gurbinsa da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.»Meaning translation ·
Saved at original quality








