Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ILIMIN AƘIDA

Daga Mahmud Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

Available in 62 languages
«Daga Mahmud Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya, Allah - Mai girma da daukaka - Zai ce da su a ranar Alkiyama idan za’a yi wa mutane sakayyar ayyukansu: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna nuna musu ayyukanku a duniya, sai ku duba shin zaku samu wani sakamako a wurin su?".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafi yawan abinda yake jin tsoronsa ga al'ummarsa: Karamar shirka ita ce: Riya; Ita ce ya yi aiki saboda mutane. Sannan ya bada labari game da ukubar masu riya a ranar Alkiyama za’a ce da su: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna aiki saboda su, ku duba shin suna mallakar saka muku da baku lada akan wannan aikin?!

Source
Ahmad ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality