Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ILIMIN AƘIDA

Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce:

Available in 62 languages
«Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadi wata kalma ni kuma na fadi wata daban, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mutu alhali shi yana kiran kishiya wanin Allah zai shiga wuta" Ni kuma na ce: Wanda ya mutu alhali shi ba ya kiran kishiya ga Allah zai shiga aljanna.»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bamu labarin cewa wanda ya karkatar da wani abu daga abinda yake wajaba ya zama na Allah ne zuwa waninSa, kamar rokon wanin Allah - Madaukakin sarki - ko neman agaji ga waninSa, ya kuma mutu akan hakan to cewa shi yana daga 'yan wuta. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya kara cewa wanda ya mutu alhali ba ya hada wani abu da Allah to makomarsa tana aljanna.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality