Hadith for the World
Imani da Allah Maxaukaki

Tauhidin Uluhiyya

14 hadiths

14 hadiths

Daga Umar Dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah - mai girma da daukaka - yana hanaku ku rantse da iyayenku", Umar ya ce: Na rantse da Allah ban yi rantsuwa da su ba tunda na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga garesu da gangan ko ina mai ciratowa (daga wanina).Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Ni ne mafi wadatar abokanan tarayya daga shirka, duk wanda ya aikata wani aiki ya hada ni da wani a aikin to Zan bar shi da shirkarsa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Umar Ibnu Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce: Bawan Allah kuma ManzonSa".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aka ce ya Manzon Allah waye mafi azirtar mutane da cetanka a ranar Kiyama? Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Hakika ya Abu Huraira na yi zatan babu daya da zai tambayeni game da wannan hadisin na farko daga kai, saboda abinda na gani na kwadayinka akan hadisi, mafi arzikin mutane da cetona a ranar Kiyama, wanda ya ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa ko ransa".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadi wata kalma ni kuma na fadi wata daban, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mutu alhali shi yana kiran kishiya wanin Allah zai shiga wuta" Ni kuma na ce: Wanda ya mutu alhali shi ba ya kiran kishiya ga Allah zai shiga aljanna.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن ابن مسعود رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «من أصابته فَاقَة فأنْزَلها بالناس لم تُسَدَّ فَاقَتُهُ، ومن أنْزَلها بالله، فَيُوشِكُ الله له بِرزق عاجل أو آجل».رواه أبو داود والترمذي وأحمد
Daga Abdullahi Dan Masud -Allah ya yarda da shi- daga Annabi ya ce: "Mafi girman Laifuffuka: yiwa Allah Shirka, da kuma amincewa Makircin Allah, da kuma yankewa daga Rahamar Allah, da kuma debe Haso daga Rahamar Allah"Abdurrazak Ya Rawaito shi
An rawaito daga Abdullahi Bn Akim -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi "Duk wanda ya danfaru da wani abu to za'a jibanta shi zuwa gare shi"Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Tarik Ɗan Ashyam al’Ashja’i, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a agare shi yana cewa: Duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya kuma kafircewa abin da ake bautawa koma bayan Allah, to, dukiyarsa da jininsa sun haramta, hisabinsa kuma yana ga Allah.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Marsad Alghanawi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance a bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wani jaki ana ce masa Ufair, sai ya ce: "Ya Mu'az, shin kasan hakkin Allah akan bayin Sa, kuma menene hakkin bayi ga Allah?", sai na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba", sai na ce: Ya Manzon Allah shin ba nayiwa mutane albishir da shi ba? Ya ce: "Kada ka yi musu albishir, sai su dogara".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, wadanne abu biyu ne masu wajabtawa? Sai ya ce: "Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna, wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta"Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai Allah Ya yardar muku da abubuwa uku, kuma Yana ƙin abubuwa uku a gareku, Yana yardar muku: Ku bauta maSa, kada ku haɗa shi da wani abu a bauta, kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gabaɗaya kada ku rarraba. Kuma yana ƙi muku: Ƙila wa ƙala, da yawan roƙo, da kuma tozartar da dukiya».Muslim ne ya rawaito shi