Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ILIMIN AƘIDA

Daga Umar Ibnu Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:

Available in 71 languages
«Daga Umar Ibnu Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce: Bawan Allah kuma ManzonSa".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana hani daga wuce gona da iri da kuma ketare iyakar shari'a a yabonsa da kuma siffanta shi da siffofin Allah - Madaukakin sarki - da kuma ayyukansa wadanda suka kebanta da shi, ko cewa shi yana sanin gaibu, ko a kira shi tare da Allah, kamar yadda Nasara suka aikata tare da Isa Dan Maryam - amincin Allah ya tabbata a gare shi -. Sannan ya bayyana cewa shi bawa ne daga bayin Allah, ya kuma yi umarni da mu fada game da shi: Bawan Allah kuma ManzonSa.

Source
Bukhari ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality