Hadith for the World
ILIMIN AƘIDA

Imani da Allah Maxaukaki

44 hadiths

44 hadiths

Daga Umar Dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah - mai girma da daukaka - yana hanaku ku rantse da iyayenku", Umar ya ce: Na rantse da Allah ban yi rantsuwa da su ba tunda na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga garesu da gangan ko ina mai ciratowa (daga wanina).Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Waqid al-Harith bin Auf - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake zaune a cikin masallaci, kuma mutane suna tare da shi, kamar yadda mutane uku suka zo, sai biyu suka zo wajan Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai daya ya tafi, ya tashi tsaye A kan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Amma dayansu, sai ya ga wani rata a cikin zobe ya zauna a ciki, dayan kuma ya zauna a bayansu. Na uku, ya yi nasarar tafiya. Lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya gama ya ce: "Shin ba zan gaya muku game da rukunoni uku ba: Daya daga cikinsu ya koma ga Allah, kuma Allah Ya ba shi. Shi kuma dayan,sai yaji kunya sai Allah ya ji kunyarsa, amma dayan sai ya bujure sai Allah ya kau da kan ga barinsaBukhari da Muslim suka Rawaito shi
عن أنس بن مالك رضي الله عنه أنَّ رَجُلاً كَانَ عِند النَبِيَّ صلى الله عليه وسلم فَمَرَّ رَجُلٌ بِهِ، فقال: يا رسول الله، أنِّي لَأُحِبُّ هَذَا، فَقَال لَهُ النَبِيُّ صلى الله عليه وسلم : «أَأَعْلَمْتَهُ؟» قال: لا. قال: «أَعْلِمْهُ»، فَلَحِقَهُ، فقال: إِنِّي أُحِبُّك فِي الله، فقال: أّحَبَّك الَّذِي أَحْبَبْتَنِي لَهُ.رواه أبو داود والنسائي في الكبرى وأحمد
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Ni ne mafi wadatar abokanan tarayya daga shirka, duk wanda ya aikata wani aiki ya hada ni da wani a aikin to Zan bar shi da shirkarsa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Yana kishi, muminima yana kishi, kishin Allah (shi ne) mumini ya zo wa abinda (Allah) ya haramta masa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Umar Ibnu Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce: Bawan Allah kuma ManzonSa".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aka ce ya Manzon Allah waye mafi azirtar mutane da cetanka a ranar Kiyama? Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Hakika ya Abu Huraira na yi zatan babu daya da zai tambayeni game da wannan hadisin na farko daga kai, saboda abinda na gani na kwadayinka akan hadisi, mafi arzikin mutane da cetona a ranar Kiyama, wanda ya ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa ko ransa".Bukhari ne ya rawaito shi
Daga Ubada - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma Annabi Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne kalmarSa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare Shi, kuma aljanna gaskiya ce haka wuta ma gaskiya ce, Allah Zai shigar da shi Aljanna akan aikin da yake akansa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadi wata kalma ni kuma na fadi wata daban, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mutu alhali shi yana kiran kishiya wanin Allah zai shiga wuta" Ni kuma na ce: Wanda ya mutu alhali shi ba ya kiran kishiya ga Allah zai shiga aljanna.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
عن ابن مسعود رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «من أصابته فَاقَة فأنْزَلها بالناس لم تُسَدَّ فَاقَتُهُ، ومن أنْزَلها بالله، فَيُوشِكُ الله له بِرزق عاجل أو آجل».رواه أبو داود والترمذي وأحمد
Daga ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa».Ibnu Majah da Baihaki da wasun su ne suka ruwaito shi
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «جَعَلَ اللهُ الرحمةَ مائة جُزْءٍ، فَأَمْسَكَ عِنْدَهُ تِسْعَةً وَتِسْعِينَ، وأَنْزَلَ في الأَرْضِ جُزْءًا وَاحِدًا، فَمِنْ ذَلِكَ الجُزْءِ يَتَرَاحَمُ الخَلَائِقُ، حتى تَرْفَعَ الدَّابَّةُ حَافِرَهَا عَنْ وَلَدِهَا خَشْيَةَ أَنْ تُصِيبَهُ». وفي رواية «إِنَّ للهِ تعالى مئةُ رحمةٍ، أَنْزَلَ منها رحمةً واحدةً بَيْنَ الجِنِّ والإنسِ والبَهَائِمِ والهَوَامِّ، فَبِهَا يَتَعَاطَفُونَ، وبها يَتَرَاحَمُونَ، وبِهَا تَعْطِفُ الوَحْشُ على وَلَدِهَا، وأَخَّرَ اللهُ تعالى تِسْعًا وتِسْعِينَ رحمةً يَرْحَمُ بِهَا عِبَادَهُ يومَ القِيَامَةِ». وعن سلمان الفارسي رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «إِنَّ للهِ تعالى مئةُ رحمةٍ فمنها رحمةٌ يَتَرَاحَمُ بها الخَلْقُ بَيْنَهُمْ، وتِسْعٌ وتِسْعُونَ لِيَومِ القِيَامَةِ». وفي رواية: «إِنَّ اللهَ تَعَالَى خَلَقَ يَوْمَ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ والأَرْضَ مئةَ رحمةٍ كُلُّ رحمةٍ طِبَاقَ مَا بَيْنَ السَّمَاءِ إلى الأَرْضِ، فَجَعَلَ منها في الأَرْضِ رَحْمَةً فبها تَعْطِفُ الوَالِدَةُ على وَلَدِهَا، والوَحْشُ والطَّيْرُ بَعْضُهَا عَلَى بَعْضٍ، فإذا كانَ يومُ القيامةِ أَكْمَلَهَا بِهَذِه الرحمةِ».حديث أبي هريرة -رضي الله عنه-: متفق عليه. حديث سلمان -رضي الله عنه-: رواه مسلم
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abin da yake ruwatowa daga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - cewa Yace: "Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci. Ya ku bayina dukkaninku ɓatattu ne sai wanda Na shiryar da shi, ku nemi shiriyata in shiryar da ku. Ya ku bayina, dukkaninku mayunwata ne sai wanda Na ciyar, ku nemi ciyarwata in ciyar da ku. Ya ku bayina dukkaninku matsiraita ne sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku. Ya ku bayina lallai kuma yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai duka, ku nemi gafarata; Zan gafarta muku. Ya ku bayania haƙiƙa ba za ku iya cutar da ni ba, ballantana ku cuceni, ba za ku iya amfanata ba, ballantana ku anfanar da Ni. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da muatnenku da aljanunku za su kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai ƙara komai daga mulkina ba. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan zuciyar mafi fajircin mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai rage wani abu daga mulkina ba. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su tsaya a bigire ɗaya su tambayeni, sai in ba kowa tambayarsa hakan ba zai rage komai daga abin da ke wurina ba, sai dai abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita kogi. Ya ku bayina kaɗai ayyukankun ne ina kiyayesu gareku, sannan in cika muku su, to, wanda ya sami alheri, to, ya godewa Allah wanda ya samu wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - da isnadi: "Lokacin da Allah ya halicci halitta, ya rubuta a cikin wani littafi, kuma yana tare da shi a kan karaga: Rahamata ta rinjayi fushina." Kuma a cikin littafin: "Ta shawo kan fushina," kuma a cikin littafin: "Na riga fushina."Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi girma a wurin Allah? ya ce: " Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka" Na ce: Lallai wannan mai girmane, na ce: Sannan wanne? Ya ce: "Ka kashe danka; dan tsoron ya ci tare da kai". Na ce: Sannan wanne? ya ce: "Ka yi zina da matar makocinka".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Musa Allah Ya yarda da shi ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Masud -Allah ya yarda da shi- daga Annabi ya ce: "Mafi girman Laifuffuka: yiwa Allah Shirka, da kuma amincewa Makircin Allah, da kuma yankewa daga Rahamar Allah, da kuma debe Haso daga Rahamar Allah"Abdurrazak Ya Rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi -tsira da Amincin Allah a gare shi- ya ce: "Wani Mutum Muslmi bai taba zama a Masallaci ba don Sallah da Zikiri, Sai Allah yayi farin ciki da shi, Kamar yadda Iyalin Matafiyi suke yi idan ya dawo Musu"Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ""Lallai Allah Ya ce: Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta zuwa gare Ni ba da wani abu kamar abinda na farlanta masa ba, bawa Na ba zai gushe ba yana kusanta gareNi da nafilfili har sai Na soshi, idan Naso shi zan zama jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da hannunsa da yake dauka da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita, kuma da zai rokeni sai na ba shi, kuma da zai nemi tsari da Ni sai Na tsare shi, kuma ban taba kai komo a kan yin wani abu kamar karbar ran mumini ba, yana kin mutuwa Ni kuma iNa ki masa wahalarsa"Bukhari ne ya rawaito shi
Idan Bawa ya Kusance ni da dani daya, sai nima na kusanceshi da tsawon Hannu, idan kuma ya kusance ni da tsawon danin Hannuwa biyu, kuma idan yazo mun yana mai tahowa sai in zo masa ina mai SassarfaBuhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Adiyyu ɗan Hatim - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakaninsu, sai ya duba zuwa daman sa ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa hagunsa shima ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa gabansa ba zai ga komai ba sai wuta wajen fuskarsa, to ku ji tsoron wuta ko da kuwa da gutsiren dabino ne".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi