Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ILIMIN AƘIDA

Daga Adiyyu ɗan Hatim - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Available in 55 languages
«Daga Adiyyu ɗan Hatim - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakaninsu, sai ya duba zuwa daman sa ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa hagunsa shima ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa gabansa ba zai ga komai ba sai wuta wajen fuskarsa, to ku ji tsoron wuta ko da kuwa da gutsiren dabino ne".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkan mumini zai tsaya a gaban Allah a ranar lahira shi kaɗai, kuma cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi magana da shi ba tare da wani wasiɗa ba, kuma babu wani tafinta a tsakaninsu wanda zai fassara zancen, sai ya yi duba ɓangaren dama da hagu saboda tsananin firgici, wataƙila zai samu hanyar da zai gudu a cikinta dan ya tsira daga wutar dake gabansa. Idan ya yi duba a ɓangaren da ke damansa ba zai ga komai ba sai abinda ya aikata na aiki na gari Idan ya yi duba a hagunsa ba zai ga komai ba sai abinda ya gabatar na mummunan aiki, idan ya duba gabansa ba zai ga komai ba sai wuta, kuma babu abinda zaisa shi kauce mata dan babu makawa daga wucewa akan siraɗi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ku sanya kariya tsakaninku da wuta da sadaka da aiki na gari, koda da wani sassauƙan abu ne kamar rabin dabino.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality