Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ILIMIN AƘIDA

Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Available in 71 languages
«Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance a bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wani jaki ana ce masa Ufair, sai ya ce: "Ya Mu'az, shin kasan hakkin Allah akan bayin Sa, kuma menene hakkin bayi ga Allah?", sai na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba", sai na ce: Ya Manzon Allah shin ba nayiwa mutane albishir da shi ba? Ya ce: "Kada ka yi musu albishir, sai su dogara".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana hakkin Allah akan bayi, da hakkin bayi ga Allah, lallai cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa Shi kadai kada su hada shi da wani abu. Kuma cewa hakkin bayi ga Allah shi ne ba zai azabtar da masu kadaitaShi da bauta ba, wadanda ba sa sanya masa abokin tarayya ba. Sannan cewa Mu'az, ya ce: Ya Manzon Allah, shin baa a yi wa mutane albishir da shi ba dan su yi farinciki, kuma su yi murna da wannan falalar ba ?? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana shi dan tsoron kada su dogara akanta.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality