Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

Available in 71 languages
«Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah Ya yi wa mutum rahama mai saukakawa idan zai siyar, kuma idan zai siya, kuma idan zai nemi biyan bashi".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da rahama ga dukkanin wanda ya kasance mai sauki mai kyauta a cinikinsa; Ba ya tsanantawa mai saye a farashinta kuma yana mu'amalantarsa da kyakkyawan halaye, Mai sauki mai kyauta idan zai siya, baya tauye mudu kuma ba ya karanta daga kimar haja. Mai sauki mai kyauta idan ya nemi biyan basukansa; ba ya tsanantawa akan talaka da mabukaci, kai yana nemansa da sauki, kuma yana jinkirtawa wanda ke cikin mawuyacin hali.

Source
Bukhari ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality