Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

Available in 45 languages
«Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a ce zai yi rantsuwa ga Allah da (Allah) Ya kuɓutar da shi".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai daga cikin mutane wanda gashin kansa a cukurkuɗe yake, ya yi ƙura, ba ya shafa masa mai, kuma ba ya yawan wanke shi, ba shi da wata daraja a wurin mutane dan haka suke ture shi a bakin ƙofofinsu, suna korarsa dan wulaƙanta shi; saidai cewa shi da ace zai yi rantsuwa akan faruwar wani abu da Allah Ya farar da abun, dan girmama shi da amsa roƙonsa, da kuma kiyaye shi daga warware rantsuwarsa, hakan saboda falalarsa da matsayinsa a wurin Allah.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality