Hadith for the World
Falaloli

Falalar Ayyuka na qwarai

16 hadiths

16 hadiths

Daga Sahl ɗan Sa'ad al-sa'idi - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, kuma bigiren bulalar ɗayanku a aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, yammacin da bawa zai yi shi saboda Allah ko jijjifi shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Hurairah - yardar Allah ta tabbata a gare shi - da isnadi: "Allah Madaukaki Ya ce: Babu wani sakamako ga bawa na mumina idan na kame darajojinsa na mutanen duniya sannan na dauke ta sai Aljanna."Buhari ne ya rawaito shi
Daga Sauban - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafificin dinaren (kudi) da mutum zai ciyar da shi: Dinarin da ya ciyar da shi ga iyalansa, da dinaren da mutum yake ciyar da shi ga dabbarsa a tafarkin Allah, da dinaren da yake ciyar da shi ga abokansa a tafarkin Allah" Abu Kilaba ya ce: "Sai ya fara da iyali, sannan Abu Kilaba ya ce: Kuma wanne mutum ne mafi girman lada kamar mutumin da yake ciyar da iyali ƙanana don ya rufa musu asiri ko Allah Ya anfanar da su da shi, kuma ya wadata su".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku maida gidajanku kaburbura, kuma kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gareni; domin cewa salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke".Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya reni 'yan mata biyu har suka balaga zai zo ranar alƙiyama ni da shi" sai ya dunƙule yatsunsa.Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Yake ɗaukaka darajoji da shi?" Suka ce: Na'am, ya Manzon Allah, ya ce: "Cika alwala a lokutan da ake ƙi, da yawan takawa zuwa masallatai, da jiran sallah bayan sallah, wadannan su ne shi ne zaman dako".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce "Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Da yawa mutum daƙal-daƙal abin tunkuɗewa a ƙofofi, da a ce zai yi rantsuwa ga Allah da (Allah) Ya kuɓutar da shi".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to, ya sadar da zumuncinsa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya ce; Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso Madina sai mutane suka fuskanto gare shi, aka ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, sau uku. Sai na zo a cikin mutane dan inyi kallo, lokacin da na gane fuskarsa, sai nasan cewa fuskarsa ba fuskar maƙaryaci bace, farkon abinda na fara jinsa ya yi magana da shi cewa ya ce: "Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
عن علي رضي الله عنه قال: سمعتُ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يقول: « مَا مِنْ مُسْلِم يَعُودُ مُسْلِماً غُدْوة إِلاَّ صَلَّى عَلَيْهِ سَبْعُونَ ألْفَ مَلَكٍ حَتَّى يُمْسِي، وَإنْ عَادَهُ عَشِيَّةً إِلاَّ صَلَّى عَلَيْهِ سَبْعُونَ ألْفَ مَلَكٍ حَتَّى يُصْبحَ، وَكَانَ لَهُ خَرِيفٌ في الْجَنَّةِ».رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد
Idan Bawa ya Kusance ni da dani daya, sai nima na kusanceshi da tsawon Hannu, idan kuma ya kusance ni da tsawon danin Hannuwa biyu, kuma idan yazo mun yana mai tahowa sai in zo masa ina mai SassarfaBuhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wata rana wani mutum yana tafiya a wata hanya, sai ya samu reshen wata ƙaya a kan hanyar, sai ya kawar da shi, sai Allah Ya yaba masa Ya kuma gafarta masa".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Dharr - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: An gaya wa Manzon Allah - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - Shin kun ga wani mutum da ya aikata aiki na gari, sai mutane suka yabe shi? Ya ce: "Wannan bishara ce ta mumini."Muslim ne ya rawaito shi
عن أبي هريرة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَن أصبح منكم اليوم صائمًا؟» قال أبو بكر رضي الله عنه: أنا، قال: «فمن تَبِعَ منكم اليوم جنازةً؟» قال أبو بكر رضي الله عنه: أنا، قال: «فمن أطعم منكم اليوم مسكينًا؟» قال أبو بكر رضي الله عنه: أنا، قال: «فمن عاد منكم اليوم مريضًا؟» قال أبو بكر رضي الله عنه: أنا، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «ما اجتمعن في امرئٍ إلا دخل الجنة».رواه مسلم
عَنْ أَبِي ذَرٍّ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَقُولُ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ: مَنْ جَاءَ بِالْحَسَنَةِ فَلَهُ عَشْرُ أَمْثَالِهَا وَأَزِيدُ، وَمَنْ جَاءَ بِالسَّيِّئَةِ فَجَزَاؤُهُ سَيِّئَةٌ مِثْلُهَا أَوْ أَغْفِرُ، وَمَنْ تَقَرَّبَ مِنِّي شِبْرًا تَقَرَّبْتُ مِنْهُ ذِرَاعًا، وَمَنْ تَقَرَّبَ مِنِّي ذِرَاعًا تَقَرَّبْتُ مِنْهُ بَاعًا، وَمَنْ أَتَانِي يَمْشِي أَتَيْتُهُ هَرْوَلَةً، وَمَنْ لَقِيَنِي بِقُرَابِ الْأَرْضِ خَطِيئَةً لَا يُشْرِكُ بِي شَيْئًا لَقِيتُهُ بِمِثْلِهَا مَغْفِرَةً».رواه مسلم