10 hadiths
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -, a cikin abin da yake hakaitowa daga Ubanngijinsa - mai girma da ɗaukaka -, ya ce: "Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, sai (allah) Mai girma da ɗaukaka ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma yana yin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo ya sake yin zunubi, sai yace: Ya Ubangiji Ka gafarta min, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma Yanayin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo sai yayi zunubin, sai ya ce: Ya Ubangiji ka gafarta min laifina, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta zunubi, kuma yanayin uƙuba a kan zunubi, ka aikata abin da ka so haƙiƙa na gafarta maka".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba ya kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, ina ƙaunar in zama ni ne shi, duk wanda ya roƙi Allah Wasila gareni, to, cetona zai tabbata gare shi".Muslim ne ya rawaito shi