Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FIƘHU DA USULU

Daga Zubair ɗan Awwam - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Available in 41 languages
«Daga Zubair ɗan Awwam - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya zo da curin itatuwa a gadan bayansa, ya saida su, Allah Ya kame fuskarsa da su, shi ne yafi alheri gare shi daga ya roƙi mutane sun ba shi ko sun hana shi».»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum ɗaya daga cikin mutane ya yi aiki kowane irin aiki ne koda zai ɗauki igiya ne, ya tattara itatuwa a gadan bayansa sai ya saida shi ya ci daga gare shi, ko ya yi sadaka da shi ya wadata daga mutane da shi kuma ya kare fuskarsa daga ƙasƙancin roƙo; shi ne ya fiye masa alheri daga ya tambayi mutane su ba shi ko su hanashi, roƙon mutane ƙasƙanci ne, mumini kuwa maɗaukaki ne ba ƙasƙantacce ba ne.

Source
Bukhari ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality