Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Available in 59 languages
«Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lalle ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yana shimfiɗa hannunSa da daddare domin mai laifi da rana ya tuba, kuma Yana shimfiɗa hannunSa da rana domin mai laifi da daddare ya tuba, har sai rana ta ɓullo daga yammacinta".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Allah - Maɗaukakin sarki - Yana karɓar tuba daga bayinSa. Idan bawa ya yi laifi da rana kuma ya tuba da daddare Allah Zai karbi tubansa, idan ya yi laifi da daddare ya kuma tuba da rana Allah Zai karɓi tubansa. Kuma tsarki ya tabbatar maSa Yana shinfiɗa hannunSa dan tuba dan farin ciki da tuban, da kuma karɓar tuban, ƙofar tuba tana nan a bude har sai rana ta ɓullo daga yammacinta dan alamtar wa da ƙarewar duniya, idan ta ɓullo to za'a kulle ƙofar tuba.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality