Hadith for the World
Tap the image to view it full size
ILIMIN AƘIDA

Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Available in 70 languages
«Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi hani game da ƙauracewar musulmi ga ɗan uwansa musulmi sama da dare uku, kowane ɗaya daga cikinsu zai haɗu da ɗayan, amma ba zai yi masa sallama ba, kuma ba zai yi masa magana ba. Mafificin waɗannan masu husumar biyun shi ne wanda zai yi ƙoƙarin gusar da ƙauracewar, kuma ya fara yin sallama, abin nufi da ƙauracewa a nan shi ne na son rai, amma kauracewa saboda haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - kamar ƙauracewa masu saɓo da 'yan bidi'a da mugayen abokai, to, wannan ba a iyakanceshi da wani lokaci, kawai ya na rataya ne da maslaha a ƙauracewar, kuma yana gushewa da gushewarta.

Source
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Download image

Saved at original quality