HA
Ladaban Shari'a
Ladaban Sallama da Neman izini
9 hadiths
Ladaban Malami da Xalibi
6
Ladaban Karatun Al-qur'ani
1
Ladaban Sallama da Neman izini
9
Ladaban Magana da kuma shiru
12
Ladaban cin Abinci da Shan Abun Sha
11
Ladabai da Hukunce Hukuncen Tafiya
4
Ladaban bacci da kuma tashi daga Bacci
3
Ladaban Mafarki
2
Ladaban Ziyara da neman Izini
3
Ladaban Atishawa da Hamma
3
Ladaban duba Mara lafiya
5
Ladaban Tufafi
8
9 hadiths
cewa Annabi - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - idan ya yi magana, zai maimaita ta har sau uku har sai an fahimce ta, kuma idan ya zo gare shi, sai ya ce masa.
Buhari ne ya rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko dutse ya tsare tsakaninsu sannan ya haɗu da shi to ya yi masa sallama kuma".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza, da amsa gayyata, da gaida mai atishawa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ke kan abin hawa shi ke sallama ga mai tafiya, mai tafiya kuma yana sallama ga wanda ke zaune, kadan kuma (suna sallama) ga masu yawa". Ga Bukhari: "Karami yana sallama ga babba, mai tafiya ga na zaune, kadan ga mai yawa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - tare da isnadi: “Bari saurayi ya gaishe da tsofaffi, masu wucewa, da‘ yan kadan a kan da yawa. ”Kuma a cikin ruwaya:“ Wanda ya hau kan mai tafiya.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Anas -Allah ya yarda da shi- "cewa shi ya wuce Yara sai yayi musu sallama, ya ce Annabi ya kasance yanayin hakan
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su -: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
كُنْتُ فِي مَجْلِسٍ مِنْ مَجَالِسِ الأَنْصَارِ، إِذْ جَاءَ أَبُو مُوسَى كَأَنَّهُ مَذْعُورٌ، فَقَالَ: اسْتَأْذَنْتُ عَلَى عُمَرَ ثَلاَثًا، فَلَمْ يُؤْذَنْ لِي فَرَجَعْتُ، فَقَالَ: مَا مَنَعَكَ؟ قُلْتُ: اسْتَأْذَنْتُ ثَلاَثًا فَلَمْ يُؤْذَنْ لِي فَرَجَعْتُ، وَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: @«إِذَا اسْتَأْذَنَ أَحَدُكُمْ ثَلاَثًا فَلَمْ يُؤْذَنْ لَهُ فَلْيَرْجِعْ»* فَقَالَ: وَاللَّهِ لَتُقِيمَنَّ عَلَيْهِ بِبَيِّنَةٍ، أَمِنْكُمْ أَحَدٌ سَمِعَهُ مِنَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ؟ فَقَالَ أُبَيُّ بْنُ كَعْبٍ: وَاللَّهِ لاَ يَقُومُ مَعَكَ إِلَّا أَصْغَرُ القَوْمِ، فَكُنْتُ أَصْغَرَ القَوْمِ فَقُمْتُ مَعَهُ، فَأَخْبَرْتُ عُمَرَ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ ذَلِكَ.
متفق عليه