Hadith for the World
Ladaban Shari'a

Ladaban Tufafi

8 hadiths

8 hadiths

Daga AbdurRahman Dan Abu Laila cewa sun kasance a wajen Huzaifa, sai ya nemi a shayar, sai wani Bamajushe ya shayar da shi, lokacin da ya ajiye ƙwaryar a hannunsa sai ya jefe shi da ita, kuma ya ce: Da badan ni na hana shi ba, ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba - kamar cewa shi ya ce: Ban aikata wannan ba -, sai dai cewa ni na ji annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Kar ku sanya alhariri (siririnsa) ko dibaji, kuma kar ku sha a cikin kofi na zinare ko na azurfa, haka nan kar ku ci a cikin farantansu, don kuwa na su ne (wanda ba muslmi) a nan duniya ku kuma zaku yi amfani da su a lahira".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya sanya alhariri a duniya ba zai sanya shi a lahira ba"Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - da isnadi: “Idan kun sa shi, kuma idan kuna yin alwala, ku fara da kwanakinku.”Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi
Daga Ali bin Abi Dalib - Allah ya yarda da shi - da isnadi: “Idan dayanku ya yi sanadi, to ya fara da dama, idan kuma aka cire shi to ya fara da hagu, kuma bari hannun dama ya kasance na farkonsu ya kwance, kuma na karshe daga cikinsu ya cire”.Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ya Ubangiji ina neman tsari da kai daga yinwa, saboda cewa ita ce mafi muni daga..., kuma ina neman daga kai daga Ha'inciBukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace ta kalli al'aurar wata mace, kuma kada wani namiji ya lulluɓa da wani mutum a cikin mayafi ɗaya, kuma kada wata mace ta lullaɓa da wata mace cikin mayafi ɗaya".Muslim ne ya rawaito shi
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu".Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shi