Hadith for the World
Ladaban Shari'a

Ladaban Malami da Xalibi

6 hadiths

6 hadiths

Daga Abu Waqid al-Harith bin Auf - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake zaune a cikin masallaci, kuma mutane suna tare da shi, kamar yadda mutane uku suka zo, sai biyu suka zo wajan Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai daya ya tafi, ya tashi tsaye A kan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Amma dayansu, sai ya ga wani rata a cikin zobe ya zauna a ciki, dayan kuma ya zauna a bayansu. Na uku, ya yi nasarar tafiya. Lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya gama ya ce: "Shin ba zan gaya muku game da rukunoni uku ba: Daya daga cikinsu ya koma ga Allah, kuma Allah Ya ba shi. Shi kuma dayan,sai yaji kunya sai Allah ya ji kunyarsa, amma dayan sai ya bujure sai Allah ya kau da kan ga barinsaBukhari da Muslim suka Rawaito shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Cewa wani balaraben kauye ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ka shiryar da ni ga wani aiki wanda idan na yi shi, zan shiga aljanna, ya ce: "Ka bauta wa Allah, kada ka hada Shi da komai, ka tsayar da sallah, ka bayar da zakkar da aka wajabta, ka azimci Ramadan" Ya ce: Na rantse da Wanda raina yake a hannunSa, ba zan yi kari akan wannan ba, lokacin da ya juya ya tafi sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda yake son ya kalli wani mutum daga 'yan aljanna, to ya yi duba zuwa ga wannan".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
عن عبد الله بن عمرو بن العاص رضي الله عنهما ، قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «إنَّ اللهَ لاَ يَقْبِضُ العِلْمَ انْتِزَاعاً يَنْتَزعهُ مِنَ النَّاسِ، وَلكِنْ يَقْبِضُ العِلْمَ بِقَبْضِ العُلَمَاءِ، حَتَّى إِذَا لَمْ يُبْقِ عَالِماً، اتَّخَذَ النَّاسُ رُؤُوساً جُهَّالاً، فَسُئِلُوا فَأفْتوا بِغَيْرِ عِلْمٍ، فَضَلُّوا وَأضَلُّوا».متفق عليه
عن عبد الله بن عمر أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «إن من الشجر شجرة لا يسقط ورقها، وهي مثل المسلم، حدثوني ما هي؟» فوقع الناس في شجر البادية، ووقع في نفسي أنها النخلة، قال عبد الله: فاستحييت، فقالوا: يا رسول الله، أخبرنا بها؟ فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «هي النخلة» قال عبد الله: فحدثت أبي بما وقع في نفسي، فقال: «لأن تكون قلتها أحب إلي من أن يكون لي كذا وكذا».متفق عليه