Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa:

Available in 48 languages
«Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ni'ima da farin ciki da kyau a duniya, kuma Allah Ya isar da shi zuwa ni'imar aljanna da ni'imarta a lahira; ga wanda ya ji zancensa sai ya haddace shi har ya isar da shi ga waninsa, sauda yawa wanda aka isarwa hadisin ya zama ya fi kiyayewa kuma ya fi fahimta kuma ya fi ikon yin istinbaɗi daga wanda ya ruwaito hadisin, sai na farkon ya zama yana kyautata hadda da dakkowa, na biyun kuma ya zama yana kyautata fahimta da istinbaɗi (tsamo hukunci).

Source
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Download image

Saved at original quality