Hadith for the World
Tap the image to view it full size
FALALOLI DA LADUBBA

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Available in 60 languages
«Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace ta kalli al'aurar wata mace, kuma kada wani namiji ya lulluɓa da wani mutum a cikin mayafi ɗaya, kuma kada wata mace ta lullaɓa da wata mace cikin mayafi ɗaya".»

Meaning translation ·

Explanation

The meaning in a few plain lines

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana namiji ya kalli al'aurar namiji, ko mace ta kalli al'aurara mace. Al'aura: Ita ce dukkanin abinda ake jin kunya daga gareshi idan ya bayyana, al'aurar namiji ita ce tsakanin cibiyarsa da gwiwoyinsa, mace dukkaninta al'aurace dangane da maza na nesa, (wadanda akwai aure a tsakanin su) dangane da mata kuwa ko maharramanta to ita zata bayyanar da abinda yake bayyana a al'adance a lokacin aikinta a cikin gida. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga kaɗaituwar namiji da namiji a tufafi ɗaya , ko ƙarƙashin mayafi ɗaya alhali suna cikin tsiraici, da kuma mace ta kaɗaita da mace a tufafi ɗaya ko ƙarƙashin mayafi ɗaya a tsiraice; Domin hakan zai iya kaiwa zuwa shafar al'aurar kowanne daga garesu, shafarta kuwa abin hanawa ne, kamar kallon al’amuran ne, kai shi ne ma mafi tsanani a hani; Saboda hakan zai iya kaiwa zuwa barna girma.

Source
Muslim ne ya rawaito shi
Download image

Saved at original quality